SHIN DA GASKE NE?

Lydia IUD bata janyo rashin haihuwa, abunda kawai takeyi shine tana bada tazarar haihuwa matukar tana cikin mahaifa. Ana cireta zaki koma kina daukan juna biyu.
Lydia IUD tana zuwa ne a ire iren samfura har guda 5 ta yadda zaki iya zaban wacce kike so, akwai yara wacce ake kira da Lydia sleek ta dace da matan da basu taba haihuwa ba.
Lydia IUD baza ta taba yiwa maigidanki lahani ba a yayin saduwar aure saboda shi gaban maigida maya isa har mahaifa a yayin saduwa. Shi ko kirtanin da yake fitowa yana da laushi sosai ta yadda shi mai gidan ma ko alamunsa ba zai jiba.
Yanayi zafin da ake ji a yayin sanyata ya bambanta tsakanin mata. Zaki iya shan ibuprofen ko paracetamol don rage zafin kafin a sa miki ita. Tafi saukin sha’ani a yayin da kike al’adarki don lokacin mahaifarki na bude ne. idan ma kin ji da radadi na dan wani lokaci ne.
Lydia IUD bata yawo a cikin jiki ballantana ma har taje kwakwalwa ko zuciya, tana zama a cikin mahaifa ne yadda kikasa kwallo a cikin bawonsa.
Za a iya sa Lydia IUD a kowane irin lokaci wanda masaniyar kiwon lafiya ce take sata. Lokacin al’adarki tafi inganci ne kawai saboda tabbacin cewa bakya dauke da ciki kuma saboda a wannan lokacin mahaifarki na bude ne ta yadda zai fi mata sauki wajen sanya miki ita.
Lydia IUD bata janyo cututtukan da ake dauka wajen saduwa, ana kwaso cuta ne idan an samu alakar aure tsakanin mutum da mai dauke da kwayar cutar, idan ana shakkan matsayin mai gida sai ayi amfani da kondom ko kororon roba.
Lydia IUD bata janyo rashin haihuwa , tana hana maniyyin namiji shiga mahaifa ne kawai sai ta haddasa rashin daukan ciki.
Lydia IUD bata janyo daukan ciki a wajen mahaifa kuma bata haddasa hakan a kashin gaskiya. Ana samun ciki a wajen mahaifa ne kawai idan maniyyin da namiji ya hadu da na mace a wajen mahaifa.
Lydia IUD bata haddasa cutar daji ko kuma ta janyo miki cutar kumburin mahaifa. Mata masu cutar nonon daji ma ba a barsu a baya ba zasu iya amfani da Lydia IUD.
 

Har yanzu baki gamsu ba?

Ku turo mana sako
zamu amsa muku.

Ku sadu damu

Ku gana da
masanin kiwon
lafiya a
kan Lydia IUD

beLydiaSmart
close

KU SA LOKACIN GANAWA

Samulydia IUD dinki

We will get back to you as soon as possible on the health provider’s availability.

Don neman Karin bayani gameda hanyoyin bada tazarar haihuwa
ku kai ziyara ga wannan shafin yanargizo www.honeyandbanana.com